Yanzu dole sai ka bayarda da Sunan Shafinka na Facebook kafin ka bu’de asusun ajiya a banki ~Cewar Sabuwar Dokar CBN.

Babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan kasuwanci da su ha’de shafukan sadarwar zamani da asusun ajiyar a matsayin karin hanyoyin tantancewa.
An bayyana hakan a cikin manyan Dokokin apex bank’s “Customer Due Diligence Regulations 2023” wanda aka fitar a Babban shafin CBN ranar Juma’a.
dokar ta kunshi Samar da adireshin dindindin (cikakken adireshin jiki), adireshin wurin zama (inda za a iya samun abokin ciniki), lambar tarho, adireshin imel, da kuma hanyoyin sadarwar zamantakewa; kwanan wata da wurin haihuwa, Lambar Tabbatar da Banki; Lambar Shaida ta Haraji; kasa; sana’a; matsayin jama’a da aka gudanar; da sunan ma’aikaci,” in ji takardar a wani bangare.
A cewar babban bankin CBN, makasudin dokar shine “samar da karin matakan tantance kwastomomi ga cibiyoyin hada-hadar kudi a karkashin kulawar babban bankin Najeriya don ci gaba da bin ka’idojin da suka dace na dokar hana safarar kudade ta MLPPA), 2022, Dokar Ta’addanci (Trevention and Prohibition) Act (TPPA), 2022 CBN (Anti-Money Laundering, Combating the Financing of Terrorism and Counting Proliferation Financing of Weapon of Mass Destruction in Financial Institutions) Dokokin, 2022 CBN AML, CFT da Dokokin CPF) da mafi kyawun ayyuka na duniya.”
Idan har bankunan kasuwanci suka aiwatar da wannan ci gaban, za a sa ‘yan Najeriya su kara asusun ajiyar su na dandalin sada zumunta zuwa ga bayanan bankin su.