Labarai
Yanzu haka Shugaba Bola Tinubu yana rantsar da Ministocinsa.


A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana rantsar da sabbin mambobin majalisar ministocin sa.
Bikin na gudana ne a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ministocin da aka nada suna karbar rantsuwar ne a haruffa bisa ga jihohinsu da kuma rukuni biyar kowanne.
Shugaban zai ba da umarninsa ne a karshen rantsuwar wanda nan take ministocin za su je ofishinsu domin ci gaba da aiki.