Labarai
Yanzu Haka Shugaba Buhari Na Kaddamar Da Wannan Kayataccen Ginin Mai Hawa 17.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yanzu haka yana aikin kaddamar da wannan ginin na hukumar tattara bayanai ta, NCDMB daga fadarshi dake Abuja.
Kayataccen ginin me hawa 17 yana garin Yenagoa na jihar Bayelsa ne kuma yana da tashar samar da wutar lantarki ta kansa wadda bata da alaka da kamfanin wutar lantarki na kasa.
Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana yanzu haka shugaba Buhari na halartar kaddamar da wannan gini daga fadarsa dake Abuja ta kafar sadarwar Zamani.