Yanzu Hukamar tsaro ta zama abin tsoro ga al’umma, ya zama wajibi a biya diyyar kisan gillar da sojoji sukayi kan ‘Yan Maulid ~Kwankwaso.
Tsohon gwamnan jihar Kano Kuma Dan takarar jam’iyar NNPP a zaben Daya Gabata na 2023 Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da kisan Yan Maulid a Kaduna ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook Yana Mai cewa Ina bakin ciki da labarin harin da jirgin sama mara matuki ya kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama a yankin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi.
Wannan lamari na harin ‘kuskure’ na iska, wani lamari ne mai cike da ban tsoro na jami’an tsaro da ke barin barnar da ba a yi niyya ba ga talakawan da ya kamata su kare a kasar nan.
Ya kamata hukumomin da abin ya shafa su tunkari wannan da dukkan ikhlasi da azama wajen ganin an yi adalci, tare da kaucewa duk wani abin da zai faru nan gaba.
Don haka, ina bibiyar sauran masu hannu da shuni wajen yin kira ga gwamnati da ta biya wa al’ummar Tudun Biri wadanda suka rasa rayukansu diyya bisa ga mugun halin da suka shiga. – RMK