Labarai

Yanzu lokacin aiki ne a jihar Kano ~Sheikh Daurawa

Spread the love

Shahararran Malamin Addinin Muslunci Sheikh Aminu ibrahim Daurawa a cikin hudubar sallar Juma’arsa na yau ya yi kira ga Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf bisa Nasarar da ya samu a Kotun Kolin Nageriya, Malami Yana Mai cewa na samu labarin Abba Gida-Gida ya yi Nasara a Kotun Kolin Nageriya to Muna Masa addu’a guda hu’du.

Na farko Allah ya bashi mashawarta na kwarai.

Na biyu Allah Yasa ya Cigaba da Ayyukan Daya dakko na alkhairi.

Na uku ya yafewa kowa ka da yazo yace zai dauki fansa akan wa’yanda ba suyi shi ba domin yanzu shi Gwamna ne na kowa idan ka samu Nasara kowa naka ne.

Na uku a mayarda hankali kan cigaban jihar Kano da ha’din kan jama’ar Kano da cigaban jihar Kano da Nasarar Kano don haka Muna Addu’a Allah ya taimaka Masa.

A yau ne Kotun Kolin Nageriya ta tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf amatsayin Halastaccen Gwamnan jihar bayan tayi watsi da hukuncin kotun daukaka Kara Court Of Appeal.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button