Labarai

Yanzu lokacin fasahar Zamani Ba dole Sai Shugaban kasa Da Mataimakinsa Suna Nageriya ba kafin gudanar da Mulki -Fadar Shugaban kasa.

Spread the love

Babu wani gibi na shugabancin kasar, duk da kasancewar Shugaban Kasa da Mataimakinsa sun kasance a kasashen waje a halin yanzu – Cewar fadar Shuganan kasa.

“Biyo bayan tambayoyin da ‘yan jarida suka yi kan wanene ke jan ragamar kasar tunda Shugaban Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa sun kasance yanzu haka a kasashen waje ‘yan Jarida sun bukaci a fayyace Masu.

Fadar Shugaban kasa ta bakin Bayo Onanuga Mai Ba da Shawara na musamman Ga Shugaban kasa Na cewa Abu ne mai muhimmanci a sani cewa Shugaban Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa suna ci gaba da gudanar da harkokin kasar sosai , duk da kasancewar su na wajen kasar Amma Babu wani gibi na shugabanci a kasar.

“Shugaba Tinubu ya fita daga kasar tun ranar 3 ga watan Oktoba domin hutu na makonni biyu, amma duk da haka, yana ci gaba da gudanar da ayyukan kasa ta hanyar wayar hannu da bayar da umarni kan muhimman al’amura na kasa. Zai dawo gida nan ba da jimawa ba kafin wa’adin hutun ya kare.

“Mataimakin Shugaban Kasa ya bar kasar a ranar Laraba zuwa Sweden a wata ziyarar aiki da ke da alaka da ayyukan kasa.

“Dukkanin hukumomin gwamnati suna aiki kamar yadda aka saba. Shugaban Majalisar Dattijai, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ministoci, da Shugabannin hukumomi duk suna kan aiki wajen tabbatar da cigaban tafiyar da mulkin kasar yadda ya kamata.

“Mun taba samun irin wannan yanayin a shekarar 2022 lokacin da tsohon Shugaban Kasa Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo suka fita daga kasar a lokaci guda. Shugaba Buhari ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 yayin da Osinbajo ya halarci jana’izar Sarauniya Elizabeth II.

“Haka kuma mun fuskanci irin wannan yanayi dai a wannan gwamnati. A tsakanin karshen watan Afrilu zuwa farkon watan Mayun bana, yayin da Shugaba Tinubu ke London, bayan ziyararsa zuwa Netherlands da Saudi Arabia, inda ya halarci taron Tattalin Arzikin Duniya, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bar kasar zuwa Nairobi domin halartar taron Shugabannin IDA21. Daga bisani ya koma Dallas, Texas, domin halartar taron Kasuwancin Amurka da Afirka da CCA ta shirya. Shugaba Tinubu ya dawo gida ranar 8 ga watan Mayu. A lokacin nan ma gwamnatin ba ta tsaya ba.

“Dokar Mulkin Kasar, wadda ta nuna dacewarta da cigaban zamani na amfani da hanyoyin sadarwa, ba ta bukatar Shugaban Kasa ko Mataimakin Shugaban Kasa su kasance a zahiri a cikin kasa a koda yaushe don su gudanar da ayyukansu.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button