Labarai

Yanzu na Gama Shiryawa domin ha’da kan Jam’iyun adawa Kuma Ina Taya Gwamna Abba murna da samun Nasara ~Atiku Abubakar.

Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alh Atiku Abubakar ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook Yana Mai cewa Hukuncin kotun koli ya nuna gagarumar nasara ga al’ummar jihohin Bauchi, Plateau, Akwa Ibom, da Zamfara kuma babu shakka nasara ce ga dimokuradiyyar tsarin mulki.

Ina taya Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano na Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) murna bisa nasarar da ya samu a shari’a. Har ila yau, wannan lokacin dake da kyakkyawar dama don sake mayar da kuduri na a kan ra’ayin na ha’de kan yan adawa wanda ke da mahimmanci don ƙarfafa dimokuradiyya a Najeriya. Ni a shirye nake kowane lokaci don in jagoranci wannan aiki, tare da yin aiki tare da manyan shugabanninmu da gwamnoninmu don ci gaban al’ummarmu.

Hukuncin kotun kolin ya tabbatar da ci gaba da gudanar da manyan tsare-tsare da jam’iyyar PDP ta kafa a wadannan jihohi.

Ina kira ga Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, Dauda Lawal na Zamfara, Barr. Caleb Muftwang na Filato, da Fasto Umo Eno na Akwa Ibom don ganin nasarar da suka samu a kotun koli a matsayin wata dama ce ta kara dagewa tare da fadada kyakkyawan shugabanci da suka rigaya ke samarwa.

Kasancewar lokacin zabe ya biyo bayanmu, ina da yakinin cewa jam’iyyar PDP za ta mayar da hankali kan muhimmiyar rawar da take takawa a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, karkashin jagorancin gwamnoninta da ni kaina. – AA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button