Yanzu yakamata ‘yan adawa su daina adawa da Tinubu domin samun cigaban Nageriya ~Cewar Gwamna Uba sani.
Gwamna Malam Uba sani na Kaduna ya Taya Shugaban Kasa Bola Tinubu murnar samun nasara a Kotun Kolin Nageriya inda Gwamna ya wallafa a shafinsa na Twitter Yana cewa Ina taya jagoranmu, Bola Ahmed Tinubu, GCFR murnar samun nasara kotun koli kan Hukuncin jiya, wannan ya kawar da duk wani shakku game da sahihanci wa’adin da al’ummar Najeriya suka baiwa Shugaban.
Wannan lokaci ne da ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa su hada kai su marawa shugaban kasa baya ganin yadda yake aiki tukuru domin fitar da Najeriya daga halin da take ciki. Kasarmu da al’ummarmu suna cikin kalubale masu ban mamaki. Bari dukanmu mu mai da hankali kan kirkira da aiwatar da hanyoyin magance matsalolinmu.
Gwamna jihar Kaduna na daya daga cikin gwamnonin jam’iyar Apc Dake Arewa maso Yammacin Nageriya.