Labarai

Yanzu Yakamata ‘yan Nageriya su dawo tsarin Dimokuradiyyar Gaskiya ~Peter Obi.

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, ya yi kira ga shugabannin siyasa da su dawo bin tafarkin dimokuradiyya na Gaskiya

Obi ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa a shafinsa na X ranar Laraba.

A cewarsa, dimokuradiyya ta wuce zabe, amma ya kasance nauyin da ya rataya a wuyan gudanar da mulki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada

Ya bukaci shugabannin Najeriya da su mutunta tare da kare hukumomin mulkin dimokaradiyya, ta hanyar bin dokokin tafiyar da mulkin kasa da kuma yin biyayya ga al’umma.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar dimokradiyya ta 2024 a ranar 12 ga watan Yuni a Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button