Lafiya

Yanzu Yanzu- An Tabbatar Da Likitoci 16 Sun Kamu Da Cutar Covid-19 A Lagos

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Sakataren hukumar lafiya ta jahar ya baiyyana cewa ma’aikatansu mutum 16 ne aka gwada wadanda suke dauke da cutar Sarkewar Numfashi wacce akafi sani da Corona Virus.

Cikin jawabin daya wallafa ya baiyana cewa adadin wadanda suka kamu a likitocin nasu yana iya zarce hakan, amma wadanda gwajinsu ya baiyyana a hannunsu sune mutum 16 a cikin ma’aikatan.

Yazuwa yanzu dai dukkan Likitocin da aka gwada wadanda suke dauke da cutar an killace su a wuraren da ake killace masu dauke da cutar a jahar ta Lagos

Hukumar ta baiyana cewa hakan yana faruwa ne saboda karancin kayan kare kai da ma’aikatan suke dashi, hakan ne yake sabbaba yawan kamuwar ma’aikatan lafiyar a Jahar ta baki daya.

A karshe ya shawarci Gwamnati data wadatasu da kayan kariyar kai daga kamuwa da cutar yayin gudanar da aiyukansu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button