Labarai
Yanzu Yanzu: Buhari ya baiwa Tinubu da Shettima Lambobin yabon GCFR da GCON

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama zababben shugaban kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasa.
An ba Tinubu ne babban kwamandan oda na Tarayyar Najeriya (GCFR) yayin da aka karrama Shettima da babban kwamandan oda na Niger (GCON).
An gudanar da bikin ne a ranar Alhamis a Abuja.