Labarai

Yanzu Yanzu Gwamna Ganduje ya tsige Salihu Tanko Yakasai bisa Zatgin Kalam Cin zarafi Ga Shugaba Buhari

Spread the love

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya dakatar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai kan wasu maganganun cin zarafi ga Shugaba Muhammadu Buhari Wanda ya yada a Kafafen sada zumuntar Zamani Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya isar da umarnin na gwamnan a cikin wata sanarwa da yammacin yau,

ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take. Ya ce duk da cewa mai taimaka wa kafafen yada labaran ya na da dama da ra’ayinsa na kashin kansa, amma a matsayinsa na mutun na Jama’a zai yi wahala a banbance tsakanin ra’ayin mutum da matsayinsa a kan al’amuran da suka shafi mulki. Don haka gwamnan ya gargadi masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da su kiyaye daga yin maganganun da za su iya haifar da rigima da ba ta dace ba

Sanarwar ta sake tabbatar da jajircewar Gwamna Ganduje ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Buhari. MALAM MUHAMMAD GARBA Hon. Kwamishinan yada labarai, na jihar Kano 11/10/2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button