Rahotanni

Yanzu Yanzu- Gwamnan Jahar Ogun “Dapo Abiodun” Yakara Wa’adin Mako Guda Na Zaman Gida.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Biyo bayan wa’adin da gwamnatin Taraiyya ta sanyawa Jahohi uku a Najeriya FCT,Lagos, Da Ogun na Mako daya, inda wa’adin nasu zai kare 4 ga watan Mayun 2020.

Gwamnan jahar Ogun ya kara tsawaita zaman gidan na mako guda gabda jahar zata fita daga cikin takunkumin kulle da shugaban kasa ya sanya mata.

Gwamnan ya baiyana cewa maimakon 4 ga wata ankara sati daya har zuwa 9 ga watan damuke ciki, inda daga bisani za’a sassauta dokar yazama daga 6 na safe har zuwa 8 na dare kafin a rufe ko Ina.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa Gwamnan ya baiyana cewa Makarantu da Wuraren Ibadu zasu zama a kulle har zuwa nan da wani lokaci, wuraren wanke gyaren jiki da filayen kwallon tamaula suma suna cikin wadanda kullen ya shafa.

A karshe gwamnan ya sanya dokar masu motar dake daukar mutum 18 zasu dawo daukar mutum 7, inda keke mai kafa uku zai rinka daukar mutum 2 kadai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button