Labarai

YANZU-YANZU: Gwamnan Katsina Dr. Dikko Radda Ya Rufe Duk Asusun Ajiyar Bankin Hukumomi Da na Kananan Hukumomin Jihar

Spread the love

YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Katsina Dr. Dikko Radda Ya Rufe Duka Asusun Ajiyar Banki Na Hukumomi Da Na Kananan Hukumomin Jihar Baki Daya

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda ya bayar da umurnin rufe dukkan asusun ajiya a bankuna na hukumomi da kananan hukumomin jihar Katsina baki daya wanda tuni bankunan jihar sunbi umurni sun rufe.

Gwamnan jihar ya bayyana cewa bazai zura ido yana kallon wasu ‘yan tsiraru suna sace kudaden jihar a banza ba, wannan dalilin yasa zai maida Asusu guda daya a fadin jihar.

Wannan hanyar na maida Asusu guda daya tana daga cikin hanyoyin rage barna da wawure kudaden jiha ba tare da tsinana wani abun kirki ba.

A wannan yanayin halin da muke ciki na kuncin rayuwa, samun Gwamnoni irinsu Gwamna Zulum da Gwamna Dikko Radda ba karamin dace bane da kuma ragewa talakawa radadin halin da suke ciki. Hatta mu haifaffun jihar Katsina duk da mun kasance bamu zaune a jihar ba karamin dadi muka jiba.

‘Yan uwa Don Allah mu saka Gwamna Dikko Radda a cikin Addu’o’inmu, Allah ya cigaba da karfafa mishi guiwa, ya bashi ikon kamanta adalci tare da sauran Gwamnonin mu baki daya.

Katsinawa ma sun samu Gwamna ZULUM a jihar su.


Comr Abba Sani Pantami,
Marubuci, Mai Fashin Baki, Dan Jarida Mai Yada Labarai A Kafofin Sada Zumunta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button