Yanzu-Yanzu: INEC Ta Bayyana Zaben Gwamnan Adamawa A Matsayin Wanda Bai Kammala Ba (Inconclusive)
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Adamawa da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Adamawa da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba.
‘Yar takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar, Sanata Aishatu Dahiru da aka fi sani da Binani ta samu kuri’u 390,275 yayin da gwamna mai ci Ahmadu Fintiri dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 421,524.
Sai dai INEC ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba saboda tazarar kuri’u.
Ya zuwa yanzu dai an bayyana sakamakon zaben gwamnoni 20. Jam’iyyar APC ce ke kan gaba da jihohi 14, jam’iyyar PDP mai jihohi biyar sai kuma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) mai jiha daya. Hakazalika hukumar zabe ta ayyana rashin kammala zaben a Kebbi yayin da aka dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna a Abia da Enugu.
A hukumance, gwamnoni tara daga cikin 11 da suka nemi sake tsayawa takara a zaben ranar 18 ga watan Maris da aka gudanar a fadin Najeriya a yammacin Afirka, INEC ta ayyana a matsayin wadanda suka lashe zaben da za su sake komawa kan karagar mulki na tsawon shekaru hudu kowanne.