Lafiya
Yanzu Yanzu-Jahar Lagos Ta Kara Sallamar Majinyata 42 Masu Dauke Da Cutar Covid-19.

Daga Haidar H Hasheem Kano
Ministan lafiya na jahar ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya baiyana cewa jaharsa ta sallami majinyata mutum 42 a yau juma’a.
Majinyatan sun hada 20 Mata inda 22 daga cikinsu kuma Maza ne.
Adadin wadanda aka sallama a yanzu yakai kimanin mutane 448 na masu dauke da kwayar cutar ta Corona Virus.