Kasuwanci
Yanzu-yanzu: Naira ta haura N755/$ yayin da CBN ya umurci bankunan da su yi ciniki cikin ‘yanci
A halin yanzu dai ana siyar da Naira akan N750-N755 kowacce dala a kasuwar masu saka hannun jari da masu fitar da kaya (I&E) ranar Laraba.
Majiya mai tushe ta shaida mana cawa babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan kasuwanci da su rika sayar da kudaden musaya kyauta bisa kayyade farashin kasuwa.