Labarai
Yanzu-yanzu: Tinubu yana ganawa da shugabannin tsaro kafin ya tafi taron G20 a Indiya.
A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da manyan hafsoshin tsaro.
Taron wanda ke gudana yanzu yasamun halartar babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, da takwaransa na sojojin ruwa, Admiral Emmanuel Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar.
Ana sa ran manyan hafsoshin tsaron kasar za su yi wa shugaban bayanin halin tsaro a kasar kafin ya jagoranci wata tawaga mai karfin gaske a yau don halartar taron shugabannin kasashen G-20 a birnin New Delhi na kasar Indiya.
Cikakkun bayanai za su zo daga baya…