Labarai

Yar gidan talaka mai tallan Goro ta zama Minista a Najeriya.

Spread the love

Hannatu Musa Musawa, da ta fito daga jihar Katsina ta fashe da kuka a yayin da ake kokarin tantance ta domin zama Minista a Gwamnatin Bola Tinubu, jiya Talata a majalisar dattawan Najeriya. Hannatu ta bada labarin yadda mahaifinsu ya taso a matsayin talaka da ke tallar Goro, daga baya ya kokarta ya samu ilmin boko.

Ganin mahaifinta Alhaji Musa Musawa ya rasu ana saura watanni 4 za a zabi ‘yarsa domin ta zama Ministar Tarayya, shiyasa ta fashe da kuka da hawaye a majalisar. Hannatu tace ta so ace mahaifinta yana da rai ya ga ‘yarsa ta zama minista, saboda sun taso ne a cikin tsananin talauci.

Rubutawa Comr Abba Sani Pantami

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button