Labarai
Yar kwankwasiyya ta Zama gwarzuwa tazo ta daya a jami’ar Mewar dake kasar India
Gidauniyar ci gaban Kwankwasiyya ce ta bai Wa Binta Sunusi tallafin karatu, don ta yi karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar kere-kere a Jami’ar Mewar ta kasar Indiya. Yanzu an girmama ta da lamba a matsayin ɗalibar ta daya mafi hazaka Jami’ar, idan baku manta ba dai a Shekarar data gabata ne dai kwankwasiyya ta tura daliban kasar Indiya domin yin Digirin na biyu a fanni kala kala..