Labarai

‘Yar Nageriya ta lashe Gasar iya girki a matakin duniya.

Spread the love

Shahararriyar Mai dafa abinci a Najeriya, Hilda Bassey, wacce aka fi sani da Hilda Baci, ta yi wani bajinta mai cike da tarihi a ranar Litinin din da ta gabata, lokacin da ta karya tarihin dafa abinci duniya na Guinness na tsawon lokacin girki da wani mutum ya yi.

Da misalin karfe 08:32 na safiyar Litinin, Baci ta yi girki na awanni 88 da mintuna 32 inda ya zarce tarihin na wani mai dafa abinci dan kasar Indiya, Lata Tondon wanda ya kafa a baya a shekarar 2019. Wanda ya rigaya ya dafa na tsawon awanni 87, mintuna 45, da dakika 00.

Baci ta fara kalubalantar gasar cin abinci na kwanaki hudu a ranar 11 ga Mayu a Amore Gardens.

Mai dafa abincin mai shekaru 27 zai ci gaba da dafa abinci don tsawaita tarihin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button