Yawan Cin Bashi Zai Durkusar da Kanana Sana’o’i Inji Lawal Ahmad.
Nayi rubutu sosai akan abubuwanda zasu biyo bayan yawan cin bashin da wannan gwamnati keyi. Daya daga Cikin abinda na fada, shine. Gwamnati zata kara farashin Man fetur dakuma daga haraji gaba kadan. Kuma hakan yanada illoli do yawa.
Wadannan illolin zasufi shafar Kananan sana’oi da kuma talaka mai-karamin Karfi. Ni Talibine kuma Mai bincike akan siyasar cigaba da kuma tattalin arzikin kasa da Kasa. Saboda haka nasan yadda Akeba, kasahe conditions kamin abasu Bashi. Wasu daga cikin conditions din sune kara farashin kayan masarufi, cire subsidy da kuma daga haraji.
Hakika ba wata kasa da nakaranta ko ziyarta da bata cin bashi, hasalima manyan kasashe irin china da America Sun gina Kasashen tattalin arzikinsu ne da Bashi. Amma banbabcin nasu dana Nigeria shine, ana cin bashine abiya albashi, akula da jindadin masu mulki, ayi bushashar gwamnati, a biya yan majalisu, asaya motocin alfarma sannan a sace.
Wata babbar matsalar itace, rashin shigar da masana lokacin tattaunawa da duba conditions din kamin saka hannu dakuma tattancewa.
A matsayina na dan kasa, zangoyi Bayan gwamnati ta ciwo bashi ta saya iri domin rabawa manoma, ta Gina masanantu, domin sarrafa albarkatun gona, ta gina storage facilities, taba yan kasuwa bashi don su saya kayan daga masana’antu sai ta gina hanyoyin titin jirgin kasa da mota da Zai hada Gonaki zuwa Kasuwa zuwa factories Zuwa sea da air ports. Wannan lissafin shine yake bukatar cin bashi kuma zangoyi bayan wannan tsarin.
Duk dayake wannan ba gwamnati bace mai jin shawara dajin korafin yan kasaba, Amma kuma yin shiru bazaiyiyuba. Akwai yiwuwar gwamnati zata cigaba da Kara kudin Mai do haraji. Idan sukayi haka kudin kayan abinci Zai karu, kudin haya MA gidaje da shaguna, da kudin magani da sauran abubuwan bukata. Rayuwa zatafi karfin talaka.
Lawal Ahmad mail bincike na akan cigaban kasa da Hulda tsakanin kasa da kasa mazaunin Babban Birnin Tarayya Abuja