Yayi Mata Fyade Lokacin Da Mahaifiyarta Ta Aiketa Kai Abincin Sallah Makwabta.

An zargi Waheed Ogundele da yiwa wata Yarinya fyade lamarin ya faru ne a yankin Ologuneru a Ibadan ta jahar Oyo.
Wani dan uwan Yarinyar wanda ya bayyana kansa a matsayin Mahmud, ya shaidawa ‘yan Jarida cewa An aiki yarinyar Takai Abincin Sallah Makobta ne, Aka tsareta Aka mata Fyade.
“Ba ta dawo kan lokaci ba kuma dole ne mu je mu duba don sanin dalilin da ya sa ta yi jinkirin Dawowa.
“Mun gan ta tana kan hanya tana zub da jini a jikin ta.
“Mun tambayi abin da ya faru sai ta ce Ogundele ya yi mata fyade.
“Mun yi kokarin Kamashi mu mikawa Hukuma, amma abokansa sun shiga tsakani kuma suka taimaka masa ya tsere,
Mahmud ya ce an gabatar da karar ne a rundunar ‘yan sanda ta Eleyele”.
Da yake la’akari da yadda ake yin fyade a kasar Nan, wani lauya, Alexander Atuchukwu, ya bukaci iyaye da su ilimantar da yaransu maza daga Illar da fyade ke Haifarwa tsakanin Al’umma.
Ya ce, “A matsayina na lauya, mun gano cewa galibin masu fyade suna neman afuwa, kuma suna juyayi suna shuga tashin hankali, lokacin da aka Gurfanar dasu a gaban Kuliya.
“Fyade shine kadai laifin da bashi da kariya a doka, kamar dai yadda kisan kai yana da kariya a cikin doka amma fyade basu da shi.
“Duk lokacin da kuka yanke shawarar yiwa mace fyade, ita ce ranar da kuka yanke shawarar lalata rayuwarta har abada Inji Shi.
Ahmed T. Adam Bagas