Labarai
Yunkurin da Gwamna Uba Sani ke yi na jawo masu zuba hannun jari a fannin hakar ma’adinai ya fara samun sakamako Mai kyau a jihar Kaduna.
Yayin da shirye-shirye ke kan gaba wajen kaddamar da katafaren kamfanin sarrafa Lithium a Kaduna, hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da Ming Xin Mineral Separation Nigeria. Ltd wanda daraktan gudanarwar kamfanin hakar ma’adanai ta kasar Sin, Ming Xin Mineral Separation Nigeria Ltd karkashin jagorancin babban daraktarta a fannin bunkasa kasuwanci, Ms Leana Lee, sun ziyarci gidan gwamnatin Jihar Kaduna na Sir Kashim Ibrahim domin yi wa gwamnan bayanin shirye-shiryen kaddamar da aikin.
wannan Yunkuri na da ƙarfin farko na Samar da metric tonnes 1500 kowace rana. Kamfanin sarrafa da aka kammala shi ne mataki na 1 na aikin. Za a ninka ƙarfin masana’antar a mataki na 2 na aikin.