
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi..
Gwamantin Tarayya Ta Kafa Wani Kwamiti Da Zai Samarwa Da Mutum 774,000 Aikin Yi.
Kwamitin wanda karamin ministan kwadago da nagartar aiki Festus Keyamo ya kaddamar zai samu jagorancin babban daraktan cibiyar ayyukan yi ta kasa Mohammed Nasir Ladan Argungu.
Hakan bai rasa nasaba da kokarin fitar da kimanin yan kasa milliyan 100 daga kangin talauci da gwamnatin ta kuduri aniyar yi.
A yayin gudanar da aikin kwamitin zai samar wa mutane akalla dubu daya aiki a kowacce karamar hukuma ta Najeriya 774, inda gwamnatin za ta rinka biyansu albashin Naira 20,000 a kowanne.
