Yunkurin Kawo Sauyi A Kasa: An Kori ‘Yan Sanda 10 a Najeriya.
Hukumar kula da Aikin Yan sanda ta Najeriya ta kori wasu manyan ajami’anta guda 10 tare da rage wa wasu takwas 8 girma sakamakon wasu laifuka da suka sabawa dokokin aikin.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani, ya fitar a Yau Litinin.
Ani ya ce an dauki matakin ne a wajen wani taro na hukumar, wanda aka shafe mako uku ana gudanarwa aka kuma kammala shi a ranar Laraba 1 ga watan Yulin 2020.
Duk da cewa dai sanarwar ba ta bayyana sunayen mutanen da abin ya shafa ba, ta bayyana cewa jami’an da aka sallama din sun hada da mutum daya mai mukamin sufuritanda SP da biyar masu mukamin DSP da hudu masu mukamin ASP.
Wani mataimakin kwamishina (DCP) da cif sufuritanda (CSP) na daga cikin wadanda aka rage wa mukami, wani mataki da ya shafi wasu masu mukamin sufuritanda hudu SP da DSP da kuma ASP a cewar sanarwar.
Ta ci gaba da cewa: Hukumar ta amince da yin hukunci mai tsanani ga jami’ai 16 da gargadi ga wasu hudun.
Shin Wannan Hukuncin Ya Dace ko Dai…?
Daga Ahmed I T. Adam Bagas