Zaɓen na ƙananan hukumomi a Kano: Mun riga mun san wadanda suka yi nasara, shi yasa muka gwammace mu yi barci mu more – Mazauna Kano.
Wasu mazauna Kano sun ce sun gwammace komawa kan gado su yi bacci maimakon bata lokacinsu wajen kaɗa ƙuri’a a zaɓukan ƙananan hukumomin da ke gudana.
Mazauna yankin wadanda suka yi magana a wajen Siyar da shayi a yankin Rijiyar zaki da ke karamar Hukumar Ungogo, sun ce zaɓen ƙananan hukumomi a kasar galibi ‘yan takarar jam’iyya mai mulki ne ke lashe shi.
Fahad Hassan ya shaida wa wakilinmu cewa zaben “wani abin kunya ne kawai da ake shaidawa.”
Wani mutum, Bashir Musa, ya ce; “Wannan wani aiki ne kawai na barnatar da kuɗin ƙasa.”
Da karfe 9:30 na safe babu kayan zaɓe kuma jami’an zaben a rumfar Tudun Fulani Jamade 1, masu jefa kuri’a sun fara komawa gidajensu.
Wani mutum a rumfar zaɓen ya shaida wa wakilinmu cewa hatta kayayyakin da ba su dace ba da aka raba a cikin makon ba su kai ga rumfar zaben ba.
Ya yi zargin cewa ba kamar sauran zaɓuka ba, a wannan karon, ba zai yi zaɓe ba kamar yadda “kowa ya san wanda ya yi nasara, kawai muna jiran sanarwar.”