Labarai
Za A Bude Masallatan Haramin Makkah Da Na Madinah Domin Gudanar Da Aikin Umarah A Wannan Watan Na Ramadan.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ce Ta sanar da Za’a bude kasar ta ga masu zuwa Umarah
Saudiyya za ta bude manyan masallatai biyu na Haramin Makka da na Annabi dake Madina ga masu zuwa ibadan Umarah a cikin wannan wata na Ramadan.
Ma’aikatar Hajji da Umarah ce ta sanar da haka, inda ta ce ana gab da bude masallan biyu inda za su cika da musulman duniya a wannan wata.
Masu karatu Ya Kukaji wannan Rahoton…?