Rahotanni

Za a yi zanga-zangar gama gari idan farashin abinci ya ci gaba da hauhawa – Sanata Ahmad Lawan

Spread the love


 
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce za a gudanar da zanga-zangar gama gari idan har bangarorin gwamnati uku ba su hada kai don rage farashin abinci da kuma karin kudin wutar lantarki ba.

Lawan na bayar da gudunmawa ne a wata muhawara kan kudirin da Sunday Karimi, sanata mai wakiltar Kogi ta yamma ya dauki nauyinsa.

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce bai kamata a dauki ‘yan Najeriya da wasa ba a halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki.

“Idan ba mu dauki matakin gaggawa kan karin farashin abinci da kudin wutar lantarki ba, ba za mu ji dadin abin da za mu gani a kan tituna ba,” in ji Lawan.

“Ba za mu iya ɗaukar mutane da rai na dogon lokaci ba.”

Tun da farko, Sanatan Kogi ta Yamma ya ce farashin kayan masarufi ya tashi da sama da kashi 300, bayan cire tallafin man fetur.

“Rashin zaman lafiya a yankunan da ake noma abinci, rashin hanyoyin mota, hauhawar farashin sufuri da ake dangantawa da cire tallafin man fetur da faduwar darajar Naira, abubuwa ne da ka iya haifar da hauhawar farashin kayayyakin abinci, kayayyakin amfanin gida. ,” inji shi.

“Mafi girman kaso na karuwar farashin kayan abinci da kayan masarufi ba wai saboda wadannan dalilai ne kawai ba, har ma da ‘yan kasuwa, da dillalai don samun riba mai yawa.”

Majalisar dattawan ta bukaci ma’aikatun gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su shawo kan matsalar.

An amince da kudirin ne bayan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya kada kuri’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button