Rahotanni

Za mu fara Alkunut matukar ba a bude filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano ba__inji Sheikh Lawan Goron Maje.

Spread the love

Babban limamin masallacin juma a na Ihya’us Sunnah da ke unguwar Gwammaja da ke jihar Kano sheikh Abubakar Lawan Goron Maje acikin khudubar sa ta wannan juma’ar ya yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin ofishin babban Ministan kula da sha’anin zirga zirgar jiragen sama akan cewa lallai ya kamata a bude babban filin tashi da saukar jiragen sama Na Malam Aminu kano dake kano. Aminu kano International Airport.

Sheikh goron maje ya bayyana cewa barin filin jirgin a rufe yana matukar ba da gudummawa wajen durkushewar kasuwancin Al’ummar jihar duba da ganin cewa mafi yawan al’ummar jihar ‘yan kasuwa ne.

Malam ya ce an bar filayen jirgin sama na wasu jihohin suna cigaba da harkokin su wannan shi yake nuni da cewa akwai wata makarkashiya da aka shiryowa jihar Kano, don haka matukar ministan bai bude filin jirgin sama Na Malam Aminu kano dake kano ba to zasu fara mika masa makamin kare dangi Na Alkunut babu dare babu rana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button