Tsaro

Za mu fatattaki ‘Yan Boko Haram da ‘Yan Bindiga kafin karshen shekarar 2021, in ji Buhari.

Buhari ya bayyana lokacin da Sojoji za suyi nasara akan ‘Yan Boko Haram da ‘Yan Bindiga.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a fatattaki mayakan Boko Haram da kuma ‘yan fashi a yankin arewa maso yamma kafin shekarar 2021 ta kare.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a lokacin Sallar Juma’a don bikin ranar tunawa da Sojojin 2021 a Masallacin Kasa.

Shugaban wanda Ministan Tsaro, Manjo Janar Magashi Salihi ya wakilta ya yi kira da a yi wa Sojojin Najeriya addu’a don ba su damar kawo karshen yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya.

Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa “wannan shekara ce ta aiki kuma za mu kammala abin da muke yi.”

“Abin da ke faruwa a kasar nan da sannu zai kare. A wannan shekarar za mu gama abin da muke yi; a yi mana addu’a domin mu sami nasara, ”in ji Buhari.

Shugaban ya ce, al’umma za ta ci gaba da tunawa da irin bajintar da sojojin suka yi, kuma za ta ci gaba da yin addu’ar Allah ya jikan wadanda suka biya wannan kima na kare mutuncin kasar.

Shugaban ya kuma bayar da tabbacin cewa walwala da jin dadi na iyalan jaruman da suka mutu, da ma wadanda ke raye za su ci gaba da samun fifikon gwamnati.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button