Siyasa

Za Mu Marawa Jam’iyyar PDP Baya Ne Domin Ta Tsamo Jihar Ondo Daga Cikin Rudanin Siyasar Da Ta Tsinci Kanta A Ciki, Cewar Jam’iyyu Guda 11.

Spread the love

Jam’iyyu 11 sun hade domin goyon bayan jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Jihar Ondo da ke tafe a ranar Asabar.

Jam’iyyun siyasan sun yi ittifakin goyon bayan dan takarar PDP a zaben, Eyitayo Jegede ne domin samar da kyakkyawan shugabanci a jihar.

Kakakin jam’iyyun kuma Shugaban jam’iyyar SDP a Jihar Ondo, Oladele Ogunbameru, ya bayyana bayan taronsu na ranar Litinin.

Ya ce za su mara wa jam’iyyar PDP baya ne domin tsamo jihar daga cikin rudanin siyasar da ta tsinci kanta a ciki.

Jam’iyyun da suka rushe tsare-tsrensu suka hade da PDP su hada da Accord Party, APGA, SDP, AAC, ADP, da sauransu.

A ranar Asabar ne za a gudanar da zaben na jihar Ondo, ’yan makonni bayan na jihar Edo, wanda jam’iyyar PDP ta lashe.

Daga:- Aliyu Adamu Tsiga

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button