Za Muyi Tattaki A Kafa Tun Daga Neja Har Fadar Shugaban Kasa Domin Muyi Zanga-zanga Akan Rashin Kulawar Da Muke Samu Daga Buhari, Cewar Matasa ‘Yan Jihar Neja.
Matasa a Jihar Neja, Zasuyi Tattaki har Fadar Shugaban kasa, Suyi Zanga Zanga…
A ranar Litinin mai zuwa 19, ga wannan Watan, Matasa a Jihar Neja sun Kuduri aniyar Yin Tattaki daga Jihar Zuwa Birnin Tarayya Fadar Shugaba Buhari domin Yin Zanga zangar Nuna rashin Jin Dadinsu Kan Nuna Halin ko Inkula da sukace Buhari yayi musu kan Matsalar Hanyoyi, Matsalar Tsaro da ta Hasken Lantarki da suke fama dasu a Jihar.
Jihar Neja dai na Fama da Rashin Hanyoyi a duk Fadin Jihar.
Duk wata Hanya da Take Karkashin Gwamnatin Tarayya a Jihar Neja ta zama tamkar Babu Ita.
Hanyoyin da suka hada Daga Minna zuwa Bidda, Suleja Zuwa Minna, Kontagora Zuwa Minna da Minna zuwa Sarkin Pawa da Sauransu Sun Koma tamkar Babu su.
Ko’odineta Mai Kula da Harkokin Matasa a Jihar, Malam Umar Muhammed ne ya Sanar da Yin Tattakin ga ‘Yan Jarida.
Ko a Makon da ya gabata Gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello, Ya gana da Shugaba Buhari Inda ya nemi gwamnatin Tarayya ta kawo agajin Gaggawa ga Hanyoyin Jihar, Amma Har Yanzu Shuru kakeji Malam. Yaci Shirwa.
Ko a Ranar da akayi Bikin munar Cika Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai, Gwamna Bello ya yi ziyarar gani da Ido Hanyar Minna zuwa Suleja Inda Gwamnan ya ce Hanyar Takoma Tamkar Kushewar Matafiya.
Daga Ahmed T. Adam Bagas