Za’a Bude Masallacin Makkah A Ranar Lahadi
Daga Haidar H Hasheem Kano
Hukumomi a Saudiyya, sun ce za’a bude masallacin Makka a ranar Lahadin nan, bayan shafe watanni uku masallacin mai tsarki na rufe sakamakon bullar annobar cutar korona.
Wata sanarwa ta ma’aikatar kula da harkokin addini da gidan talabijin din kasar na Al-Ahbariya ya fitar a jiya Juma’a, ta ce za’a bude masallatai a Makkah, domin baiwa jama’a damar gudanar da ibada.
Matakin dai na zuwa ne makwannin kadan kafin fara aikin hajjin bana da za’a fara a watan Yuli mai zuwa.
Har yanzu dai Saudiyya ba ta fayyace wa duniya ba ko za’a gudanar da aikin hajjin na bana ba ko kuma a’a.
A karshen watan Mayu, Saudiyya ta bada umarnin sake bude masallatai a fadin kasar, amma da sharadin daukar matakai kariya daga cutar korona, saidai banda masallaci mai tsarki na Makkah.
Tuni dai wasu kasashen musulmi irinsu Jamhuriyar Nijar, suka ce sun hakura da aikin hajjin na 2020, sakamakon annobar korona data dagula al’amuran duniya.
A Saudiyya dai mutane sama da 150,000 ne aka tabbatar sun harbu da cutar korona, yayin ta yi ajalin 1,200.