Labarai

Za’a fara aikin Gina kauyen Tudun Biri da Jirgin sojoji ya yi kuskuren kashe ‘yan Maulidi nan da Sati biyu masu Zuwa – Uba Sani

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce gwamnatin tarayya za ta sake gina al’ummar Tudun Biri a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna wanda Jirgin yaki mara matuki na soja ya jefa bama-bamai cikin kuskure a watan Disambar da ya gabata.

Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana hakan ne a ranar Asabar da ta gabata yayin da yake jawabi ga taron kwamitin zartarwa na kasa da kwamitin ayyuka na kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya a jami’ar jihar Kaduna (KASU).

Ya yi alkawarin bai wa kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya filaye domin gina jami’a.

Da yake mayar da martani ga jagoran kungiyar Musulunci ta kasa, wanda tun farko a jawabinsa ya bukaci a gaggauta cika alkawuran da aka dauka wa al’ummar Tudun Biri, Gwamna Sani ya ce ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kwanaki biyar da suka gabata kan alkawurran da suka dauka. gwamnatin tarayya don sake gina Garin Tudun Biri.

Ya bayar da tabbacin cewa za a gina gidaje, asibitoci, makaranta, kasuwa da ofishin ‘yan sanda a cikin al’umma a karkashin aikin sake gina Tudun Biri da gwamnatin tarayya za ta yi.
A cewar gwamnan, “Kwanaki biyar da suka gabata na gana da shugaban kasa kan bukatar a gaggauta sake gina Tudun Biri, sannan shugaban ya yi gaggawar kiran mataimakin shugaban kasa, muka tattauna kan batutuwan kuma shi (shugaban kasa) ya tabbatar min da cewa za a fara aikin. nan da sati biyu.

Gwamnan wanda ya bayyana cewa an kafa wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakiyar gwamna Dr Hadiza Balarabe domin gudanar da rabon tallafin da aka yi wa al’umma, ya kuma bada tabbacin cewa za a yi wa al’ummar yankin Tudun Biri adalci.

Ya ce, a bangaren gwamnatin jihar Kaduna, ta yi jinyar duk wadanda suka jikkata 75 da suka samu raunuka sakamakon wannan mummunan lamari, tare da ba su agajin jin kai, yayin da aka kwantar da su na tsawon kwanaki 17 a cibiyar mata da kananan yara ta jihar kafin a ba su dama su tafi gida.

Da yake magana kan aikin Jami’ar da Fityanul Islam ta gabatar, Uba Sani ya ba da tabbacin cewa zai ware fili domin hakan a ranar Talata mai zuwa, kamar yadda ya yi alkawarin tallafa wa shirin kungiyar na gina gidan marayu a Kaduna kasancewar babban birnin Arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar Fityanul Islam na kasa Sheikh Muhammad Arabi Abdul Fathi ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta aikin sake gina kauyen Tudun Biri.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wa maniyyatan da ke shirin tallafa musu ta hanyar bayar da tallafin kudin aikin Hajji bisa la’akari da hauhawar farashin da aka samu wanda ya sanya aikin Hajjin 2024 ya tashi.

Shugaban na addinin Islama ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohi 36 da su yi kokarin inganta tattalin arzikin jihohinsu, inda ya yi nuni da cewa karuwar laifukan da ake samu a baya-bayan nan ya samo asali ne sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button