Labarai
Za’a kafa Hukumar tace fina finai da wakoki a jihar katsina ~Gwamna Dikko radda
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya gana da kungiyoyin mawaka na jihar Katsina, a inda ya dauri aniyar Kafa hukumar tace wakoki da fina-finai da sauran ayyukan fasaha domin tsabtace sana’o’in.
A yammacin ranar Juma’a ne 22 ga watan Satumba 2023, gamayyar kungiyoyin mawaka da masu shirya fim na jihar Katsina suka kaima Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda ziyara a fadar gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Kungiyoyin sun kawo ziyarar dai domin jaddada goyon bayan su da kuma fatar alkhairi a bisa kokarin da Gwamnan ke yi wajen ganin Jihar Katsina ta ci gaba a fannoni daban-daban.