Za’a samu katsewar wutar Lantarki na kwana Uku 3 a Garin Mararaban Nyanya dake Abuja da Jihar Nasarawa.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya ce kwastomomin su a sassan Mararaban Abuja da Jihar Nasarawa da kewaye za su fuskanci katsewar wutar lantarki na Tsawon kwanaki uku tsakanin 3 ga Janairu, zuwa Janairu 6.
Mista Oyebode Fadipe, Manajan AEDC, Sadarwa na Kamfanin, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi
“Abokan cinikinmu a wadannan yankuna da ke karkashin Mararaba: Aso Pada, Mararaba Guruku, Kauyen Aku, Kabayi, wani bangare na hanyar Abacha zuwa kusurwar Sharp, kasuwar Orange, Abbatoir.
“Sauran sun hada da Tudun Wada, NIMCO Qtrs, Abacha Road, GT Bank, Polaris Bank, First Bank, Zenith Bank, Boundary Road, Custom Qtrs 1 & 3, overhead tank da kewayensa.
“Ana sanar da su cewa za a katse samar da wutar lantarki ga gidaje da ofisoshi daga yau, 3 ga Janairu, zuwa Janairu 6, 2020,” in ji shi.
A cewarsa, katsewar ta samo Asalin ne don ba wa kungiyar fasaha ta AEDC damar maye gurbin dukkan bangarorin masu kuka da 2X15 Mega Volt Ampree (MVA), 33/11 Kilo Volt (KV) Inj. S / S J22 a Mararaba.
AEDC, ya nemi afwar da fahimtar masu amfani a cikin yankunan da aka ambata a baya.
Amma, ya tabbatar wa kwastomomin cewa aikin gyaran an yi shi ne da nufin inganta ayyukan AEDC a gare su.
“Muna nan a shirye don taimakawa ta hanyar tambaya ta kowace hanyar tuntubar mu. “In ji shi. (NAN)