Zababben Gwamnan Jihar Zamfara Ya Nada Kwamitin Karbar Mulki Mai Mambobi 60
Mataimakinsa ya bayyana cewa, kwamitin ya kunshi masu fasaha na yanzu da masu rike da mukaman gwamnati da suka yi ritaya, da kuma kwararru daga kowane bangare na rayuwa.
Zababben gwamnan jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, ya kafa kwamitin karbar mulki mai mutum 60 domin share fage na rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Mai taimaka wa zababben gwamnan kan harkokin yada labarai, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa an dora wa kwamitin alhakin hulda da gwamnatin Gwamna Bello Matawalle mai barin gado.
An nada tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda Mohammed Abubakar a matsayin shugaban kwamitin, yayin da Dr. Hamza Mohammed zai kasance a matsayin Sakatare.
Haka kuma, sauran mambobin kwamitin sun hada da tsohon shugaban ma’aikata a jihar, Mujitaba Isah Gusau; Col. Bala Mande (rtd.); Farfesa Abubakar Aliyu Liman; Nura Ibrahim Zarumi, da ‘yan majalisar wakilai na kasa masu rike da madafun iko da dai sauransu.
An ce kwamitin ya kunshi masu fasahar zamani da masu rike da mukaman gwamnati da wadanda suka yi ritaya da kuma kwararru da masana daga kowane bangare na rayuwa.
Sanarwar ta kara da cewa babban aikin kwamitin shi ne samar da tsarin tuntuɓar juna tare da samar da tsaftatacciyar hanyar sadarwa tare da gwamnati mai barin gado don samun sauyi cikin sauƙi.
Idris ya kara da cewa kwamitin zai hada kan ma’aikatu da hukumomin gwamnati (MDAs) tare da duba kudaden gwamnatin mai barin gado tare da mai da hankali kan rasit, kadarori, da lamuni da dai sauransu.
Ya kuma kara da cewa nan gaba kadan za a bayyana ranar da za a kaddamar da kwamitin karbar mulkin ga Gwamna.