Siyasa

Zabar Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa ya nuna muradin mutane – Buratai

Spread the love

Tsohon babban hafsan soji mai murabus Laftanar Janar Tukur Buratai yace fitowar zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna muradin yan Najeriya.

Mista Buratai, tsohon jakadan Najeriya a jamhuriyar Benin kuma jigo a jam’iyyar APC, ya taya Mista Tinubu murna a wata sanarwa a ranar Litinin.

Ya ce nasarar da tsohon gwamnan Legas ya samu a fili ya nuna ra’ayin jama’a.

Mista Buratai ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) karkashin jagorancin Mahmood Yakubu bisa jagorancin gudanar da zabe a kasar dake da dimokuradiyya mafi girma a nahiyar Afirka.

“Bari in fara da taya ’yan Najeriya masu kada kuri’a da suka fito a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 domin gudanar da ayyukansu na jama’a kuma suka zabi Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa. Hakan na nuni ne da nufin jama’a,” inji shi.

Tsohon hafsan sojin ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su zabi dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC a fadin kasar nan a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a yi a ranar 18 ga watan Maris.

Ya bayyana cewa kuri’ar dukkan ‘yan Najeriya na da ikon kawo sauyi da kuma tabbatar da zabi na hikima da aka yi a lokacin zaben shugaban kasa.

“A halin da ake ciki, na ce da dukkan nauyin da ya rataya a wuyanmu cewa makoma tamu ta tabbata a karkashin sabon fata, hangen nesa da manufar Asiwaju Bola Tinubu. Na yi amanna cewa zababben shugaban kasa mutum ne mai iya aiki, tausayi, hangen nesa, da duk abin da ake bukata domin kai Nijeriya ga kasar da aka yi alkawari,” Mista Buratai ya bayyana.

Tsohon hafsan sojin ya kara da cewa, “Saboda haka, ina karfafa wa dukkan ‘yan Najeriya kwarin gwiwa da su zabi jam’iyyar APC a zaben gwamna mai zuwa a matakin jihohi domin jam’iyyar APC ta samu rinjaye a dukkan matakai. Kada ku kasance cikin ’yan adawa marasa rinjaye, tunda dama muna da APC a tsakiya.”

Buratai ya bayyana cewa an samu ci gaba a matakin tarayya inda Tinubu ya zama zababben shugaban kasa daga jam’iyyar APC.

“Saboda haka, don aiwatar da manufofi masu inganci, ci gaban’ tsaro da ci gaban kasarmu, kuma ku zabi APC a matakin jihohi. Najeriya za ta yi girma da yardar Allah,” inji shi.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button