Zaben Edo:Jam’iyyar PDP Ta gargadi Adams Oshomole.
Kungiyar kamfen din jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP,NCC, a zaben gwamna Edo, ta shawarci tsohon shugaban jam’iyyar na kasa baki daya, APC, Adams Oshiomhole da kar ya kuskura ya yi maganar da zata haifar da Hatsaniya a Zaben Gwamnan Edo.
Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin yakin neman zabe ya shawarci Oshomole, a wani taron manema labarai Jiya Litinin a Abuja.
“Muna kara tsawatarwa Adams Oshiomhole da ya daina wuce gona da iri game da maganar Edo, da al’umma kawai saboda shi da dan takarar sa ba su da wata hanyar da za su tallata wa mutanen Edo Kansu.
“Oshiomhole ya kamata ya tuna cewa ana kiran Edo bugun zuciyar al’umma kuma bai kamata ya haifar da rikici wanda zai haifar da tasirin gaske ga sauran sassan kasarmu ba.”
Ahmed T. Adam Bagas