Siyasa

Zaben Fidda Gwani A Edo: Kallo Ya Koma Sama.

Spread the love

Wakilai 2,229 ne, ake sa ran za su yanke hukunci wanda zai fito a matsayin Dantakarar Gwamna a jam’iyyar PDP, wanda aka shirya gudanarwa ranar 19 ga Satumabar, 2020.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Mista Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan, a Abuja, ranar Laraba.

Ya ce jam’iyyar za ta bi doka a yayin gudanar da zaben.

Ologbondiyan ya kuma ce, “Dukkanin kayan aikin da za ayi amfani dasu yayin zaben tuni suka isa jihar”.

Za’a gudanar da zaɓen cikin kulawa da ka’idodin rigakafin COVID-19.

Wakilan Kwamitin Zaben na fidda gwani tuni suka kasance a Benin don gudanar da aikin.

Tun da farko dai mutane hudu ne suka karbi tikitin tsayawa takarar.

Daga baya kuma sai aka sami kari da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, sauran masu neman takarar sune Gideon Ikhine, Ogbeide-Ihama da Kenneth Imasuagbon.

Rahotanin sun nuna cewa biyu daga cikin wadanda suka nemi tsayawa takarar sun janye, sun marawa gwamna Obaseki baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button