Zaben Gwamna: El-Rufai ya mamaye rumfar zabensa, ya doke PDP
Dan takarar APC ya samu kuri’u 257 yayin da PDP ta samu kuri’u 81 a zaben gwamna.
‘Yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi nasara a rumfar zaben gwamna Nasir El-Rufai a zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a Unguwan Sarki 024, inda ya kada kuri’arsa a ranar Asabar.
Shugaban hukumar zaben, Haruna Shafiu, wanda ya bayyana sakamakon zaben, ya ce dan takarar APC ya samu kuri’u 257 yayin da PDP ta samu kuri’u 81 na zaben gwamna.
Ya sanar da cewa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta samu kuri’u biyu, yayin da ADP ta samu uku, PRP ta samu takwas, sai kuma kuri’u takwas marasa inganci.
Yayin da APC ta samu nasara a mazabar 026 da ke kusa da inda Mista El-rufai ya kada kuri’a, da kuri’u 146, PDP ta samu kuri’u 61.
Shugabar akwatin zabe mai lamba 026, Maryam Abubakar, wadda ta sanar da sakamakon zaben, ta ce jam’iyyar NNPP ta samu kuri’u biyu yayin da jam’iyyar Labour ta samu kuri’u uku, uku kuma ba su da inganci.
(NAN)