Labarai

Zaben Gwamna: Gwamnatin Kano Ta Dage Dokar Hana Fita Daga Safiya Zuwa Magariba

Spread the love

Gwamnatin jihar ta kuma godewa al’ummar jihar bisa hadin kan da suka bayar a lokacin dokar hana fita.

Gwamnatin jihar Kano ta dage dokar hana fita daga wayewar gari zuwa magariba da ta saka sakamakon tashe-tashen hankula dangane da sakamakon da ake jira na zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin da ta gabata, “An yanke shawarar dage dokar ne bayan an yi nazari sosai kan lamarin da kuma kwanciyar hankali a fadin jihar.”

Ya yi kira ga bankunan kasuwanci, ma’aikatan gwamnati, da al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Ya kara da cewa “Muna kira ga jama’a da su ci gaba da gudanar da sana’arsu ta halal ba tare da tsoron cin zarafi ko tsangwama ba.”

Kwamishinan ya kuma godewa al’ummar jihar bisa hadin kan da suka bayar a lokacin dokar hana fita.

“Mun yaba da hadin kan jama’a a lokacin dokar hana fita. Muna rokon su da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali,” inji shi.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan jihar ta baiwa jama’a tabbacin tsaron lafiyarsu, tare da gargadin masu tayar da kayar baya da su kau da kai daga jihar.

“Mun baza jami’an mu a fadin jihar domin tabbatar da doka da oda. Duk wanda aka kama yana haddasa fitina za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada,” in ji kwamishinan ‘yan sandan jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button