Zaben Gwamna: Kotu ta umarci INEC da ta ba da damar yin amfani da katin zabe na wucin gadi

A ranar Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, (INEC) da ta ba da damar yin amfani da katin zabe na wucin gadi, (TVC) a zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da za a yi ranar 18 ga Maris.
Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da yake yanke hukunci a karar da wasu ‘yan Najeriya biyu suka shigar na neman a yi amfani da TVC a babban zaben kasar ba tare da katin zabe na dindindin ba, (PVCs).
Mai shari’a Egwuatu ya ce an bayar da wannan umarni ne a kan cewa masu shigar da kara sun yi rajista da kuma kama su a ma’adanar bayanai na INEC.
“An ba da umarnin tilasta wanda ake kara (INEC) da ya ba masu kara damar kada kuri’a ta hanyar amfani da katin zabe na wucin gadi da wanda ake kara ya bayar, an ga bayanan wadanda suka shigar da karar a cikin rumbun adana bayanan masu kada kuri’a na kasa.
“Wannan kotu ta bayyana cewa wadanda suka shigar da karar sun cika dukkan sharuddan da ake bukata na yin rijistar, saboda haka an kama su a cikin babban ma’adanar bayanai na wadanda ake kara (INEC) da kuma littafin, bugu na takarda ko kwafi na rijistar wanda ake kara. na masu kada kuri’a, masu shigar da kara suna da damar kada kuri’a ta amfani da katin zabe na wucin gadi a babban zaben 2023 mai zuwa,” inji alkalin.
(NAN)