Zaben Gwamnan Anambra ‘Yan Takarar PDP 12 kowa Halinsa ya Ceceshi~ PDP Anambra.
Shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar Anambra, Cif. Ndubuisi Nwobu yace a Zaben Fidda gwani Na Dan takarar kujerar gwamnan jihar Ba maganar Siyasar Uban gida kowa tasa ra fiddashi.
Yaci gaba da cewa “wakilan jam’iyyar ne kadai zasu yi zaben fidda gwanin Su zabi mutum mai Nagarta ba, ba mutum Domin yasan wani babba a Jiha ko kasa ba.
Nwobu yayi wannan jawabi ne ga manema labarai Jiya talata a Awka babban birnin Jihar.
Yace kawo yanzu jam’iyyar tana da ‘Yan Takarar gwamna Har mutum 12 Wanda Jam’iyyar ta amince dasu a zaben da za’ayi a Shekara ta 2021.
Yace ya godewa Uwar Jam’iyyarsu ta Kasa da ta Shiyya kan yadda ta Chanza Tsarin Kwamitin Gudanarwa ta Jam’iyyar a Jihar.
Sannan ya shawarci Shuwagabannin Shiyya ta Jam’iyyar Inda yace Su Tsaya kan Aikinsu Kar Shugaban Shiya ya shiga aikin Shugaban Jiha.
Daga bisani yace Wakilan Jam’iyyar da zasu yi zaben Fidda gwani su zabi Wanda zai yi aiki kar subi Kudi ko Babbar Riga, su zabi Chancanta Inji Shi.
Ahmed T. Adam Bagas