Zaben Ondo;- Gwamnan Kano Ganduje Ya Tashi daga Abuja zuwa Ondo.
A dai dai lokacin da Zaben Gwamnan Jihar Ondo ya rage kwanaki 2, Yau Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya Tashi daga Filin Sauka da tashin Jirage na Abuja zuwa Ondo, a Kokarinsa Na Shirye shiryan Zaben Ranar Asabar mai Zuwa.
Ganduje, wanda ya samu Rakiyar Daraktan Kafendisa a shekarar 2019, Alhaji Nasiru Ali Koki, Mai taimakinsa na musamman Alhaji Salihu Tanko Yakasai, Barr. Audu Fagge, Alhaji. Faruk Mudi, DG. Uba Danzainab, Dan Shi Engr. Abba Umar Ganduje da Sauran Mukarraban Gwamnan Kano ne suka Nufi Ondon Yanzu Haka.
Tun a Ranar Asabar da tagaba ne dai Tsohon Gwamnan Jihar Kano Engr. Rabiu Musa Kwankwaso ya Sauka a Ondo, Domin Taya dan Takarar Gwamnan Jihar A Jam’iyyar PDP yakin neman Zaben a Jihar.
A wannan Taron da Kwankwason yayi a Ondo ne Wasu Masana ke Ikirarin Cewar Kwankwaso ne Dan Siyasa mafi Farin Jini a Nahiyar Afrika.
Zaben na Ondo da yahada Manyan ‘Yan Siyasar Jihar Kano za’a yi Zaben ne Ranar Asabar 10-10-2020.
Kan Wannan zaben ne Shugaban Rundunar Yan Sandan Kasar, IGP. Muhamman Adamu, Ya tura ‘Yan Sanda sama da dubu 30 Jihar domin gudanar da zaben.
Allah Yasa ayi Zaben Lafiya a gama Lafiya, Ya Baiwa mai Rabo Nasara.
Ahmed T. Adam Bagas