Zaben Shugaban Kasa 2023 Gwamna yahaya Bello yayi magana Kan maye gurbin Buhari
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a ranar Litinin ya ce baya son ya shagala da kiraye-kirayen da ake yi masa na ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.
Da yake magana ta bakin Babban Sakatarensa na yada labarai, Nnogwu Sani Mohammed a taron tsaro da tattalin arziki da ke gudana na kungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai, Gwamnan ya ce “ya maida hankali ne kan isar da umarnin sake gina jihar Kogi.”
A cewar Bello, “karfin gwamnatin sa na dakile rashin tsaro a jihar ta Kogi da kuma karfafa matasa ta hanyar neman goyon baya har ya kai ga kiraye kiraye” na ya tsaya takarar shugaban kasa ya zo 2023 amma ya ci gaba da cewa “baya son ya shagala da” irin wadannan kiraye-kirayen .
Gwamnan ya yi kira ga mutane da su ba shi goyon bayan da ake bukata don isar da wa’adinsa na biyu ga mutanen Jihar Kogi.
Bello ya ce “batun shugabancin 2023 bai kamata a sa shi a gaba ba kuma ya zuga ‘yan siyasa,” in ji shi.
Ya tabbatar wa mutane cewa ya maida hankali kan alkawuran da ya dauka na inganta tsaro da samar wa matasa aikin yi a jihar.
Ku tuna cewa Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce akwai kira mai jan hankali ga Bello, da ya tsaya takarar Shugaban kasa a zaben 2023
Fanwo ya fadi haka ne yayin da yake nuna tallan yakin neman zaben Yahaya Bello a shafinsa na Twitter.
A cikin kamfen din yakin neman zaben da aka yada, ‘yan Najeriya da dama sun gamsu da ganin Bello a matsayin shugaban kasa na 2023 wanda zai iya maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari.