Zaluncin Jam’iyar APC akan Talakawan Nageriya ba zai Musultu ba -Atiku Abubakar
APC ta caccaki shugabannin da suka shude kan farashin man fetur, amma yanzu gwamnatin ta na sayar da Naira 900/Lita – Atiku ya roki jihar Edo da ta kada kuri’a cikin hikima.
Ya bayyana cewa zaluncin APC da rashin kula da halin da talakawa ke ciki bai misaltuwa, ya kara da cewa kada kuri’a ga APC “kuri’a ce ta ci gaba da zullumi da yunwa da fidda rai.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zaben jam’iyyar All Progressives Congress a zaben gwamnan jihar Edo da za a yi ranar Asabar, zai zama nuni ga wahala da Yan Nageriya ke fuskata
Atiku wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta caccaki shugabannin da suka shude kan karin farashin man fetur, inda ya ce Yanzu ana shugabancin zamanin da farashin man fetur ya haura Naira 900 kan kowace lita.