Labarai

Zama Daya Sanata Uba Sani Ya Magance Matsalar AMCON

Spread the love

A yau Shugaban kwamitin Bankuna Inshora da sauran harkokin kudade a Majalisar Dattijan Nageriya Sanata Uba Sani tare da Cibiyar kula da kadarorin cikin gida da gidajen Nageriya Asset Management Corporation Of Nigeria(AMCON) sun gabatar da wani taro mai mahimmanci a Hotel din Chelsea dake abuja domin magance wasu manyan Matsalolin da suka addabi Cibiyar da kuma sauran harkokin bashika.

Sanata Uba Sani Yace zaman Nasu na yau ya bawa Kwamitin da Cibiyar ta AMCON samun damar zurfafa tunani kan mahimman batutuwa tare da samun damar kawo cigaba duba tare sanin hanyoyin da zasu bi domin habbaka harkokin Hada-hadar kuɗade musamman ma harkar banki tare da samun damar rage hauhawar yawan kudin ruwa na wasu bashikan (NPLs) Sanatan yace Hakan nan kuma zaman ya bamu damar magance matsalolin da sukayima AMCON; katutu a wuya a bangaren manufofin Hukumar domin sanin hanyar da dawo da kadarorinta da suka lalace a wannan lokacin na Annobar cutar Corona Virus COVID-19.

Har’ila Yau Mahalarta taron sun yi la’akari da yadda cutar ta COVID-19 Tayi tasiri ga Cibiyar ta AMCON da kuma manyan matakan da dole ne a sanya su domin sake fasalin cibiyar da dabaru ta yadda Cibiyar za ta taka rawar gani wajen taimakawa da inganta harkar hada-hadar kudade a Najeriya.
Mahalarta sun nuna damuwarsu kan yadda mutane suke nuna wayon su tare da rike bashi basu son biya wanda yanzu haka kyasa kyasai da dama suna kotuna tsawon shekaru da yawa ana fama, Cibiyar ta AMCON tace hakan ba karamin koma baya bane game da tattalin Arzikin Nageriya.

Har’ila yau AMCON Ta yi kira ga majalisar ta kasa da ta fito da wasu ka’idoji na musamman a majalissar wanda zai sa Jama’a su daina wahalar da Cibiyar wajen dawo da kadarorinsu Ha zalika kuma Cibiyar ta nuna gamsuwarta game da kudurin da majalisar dattijai ta dauka na kawo gyare gyare a harkokin bankunan da sauran hukumomin cibiyoyin hada-hadar kudade da kuma sake aiwatar da dokar Bankuna da Sauran Masana’antu na Kasa da sauran batutuwan na musamman a Shekarar 2020.

A Karshe Cibiyar ta bayyana farin cikinta a tare da imanin cewa wannan matakin na Majalisar Dattijan Nageriya zai taimaka kwarai da gaske wajen kawo karshen Matsalolin su…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button