
Wani faifan bidiyo da ke zagaye yanar gizo ya nuna wasu baƙi a wurin ɗaurin aure an basu ba su Garri da gyaɗa cikin ruwan tsamo tsamo suna habzi dashi.
A cikin bidiyon, an ga gungun samarin da suka taru a teburin suna cin jiƙaƙƙen garin da gyaɗa maimakon shinkafa-kaza samfurin jollof shinkafa yar gwamanti da aka saba da ita.
Wannan baƙon abu ne wanda ba’a saba jin irin sa ba, inda ake ba wa baƙi jiƙaƙƙen garri da gyaɗa.

Kamar yadda rubutun bidiyon ya nuna, an bada gari ne a maimakon shinkafa-kaza samfurin ta tsotse saboda tsadar shirya shinkafa ga baƙi, inda aka ce wannan yana hana ku yin bikin aure, yi amfani da Garri a maimakon shinkafa-kaza.
Kalli Bidiyo anan 👇


Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru